Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yayi fice wajen sarrafa karafuna zuwa launuka daban daban a kowanne mataki a fadin kasar nan har ma da kasashen ketare.
Kamfanin ya kasance shi ne na farko da yayi amfani da karfe wajen zana siffar mutum a acikin dukkanin kamfanonin sarrafa karfe dake yankin arewacin Najeriya.
Idan aka duba wannan hoton za aga cewa Kamfanin ya zana hoton tsohon mataimakin shugaban kasa takarar shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar.
Wannan kamfani a shekarun baya ba iyaka hoton Atiku Abubakar ya zana ba, ya zana hotunan mashahuran mutane a kasar Najeriya da suka hadar da sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau da sauransu.
Kamfanin yana amfani da karfen wajen zana hotunan mutane Don hana lalata shi ko yagawa Kamar yadda ake yiwa fastotocin yan siyasa inda suke saurin lalacewa.
Wannan maganar zana hoto a jikin karfe wannan kamfani ya yi tunatarwa ne ga dukkanin mutumin da yake son a zana hotonsa ko hoton mai gidansa musamman yadda zaben shekarar 2027 ya karato to yazo kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works domin a sharemasa hawayen sa.




