Contact Info

Sanin Aiki da Gogewa Yasa Kamfanin Afuwa Welding Works Yayi Fice Kan Aikin Sarrafa Karfe.

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance gogagge kuma mai ayyuka masu nagarta a dukkanin fadin Najeriya dama nahiyar Afrika baki daya.

Wannan kamfani ya yi shuhura sannan ya shiga kunnuwan al’umma bisa kwashe shekaru masu yawa da yayi a duniyar sarrafa karfe wajen sauyamasa launi domin komawa ko wanne iri ne.

Wannan aiki da kuke gani tare da ma’aikatan mu suna gudanar dashi inda suka saka manyan karafuna a gaba daga sashen waldar kamfanin, kuma ayyuka masu nagarta gami da inganci.

Wannan kamfanin ya kasance yana da ruwa da tsaki akan ko wanne irin karfe wajen sarrafa shi kamar yadda mamallakin kamfanin yake fada wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani.

Wannan kamfani ya kasance a kowacce jiha a fadin tarayyar Najeriya babu inda baije ya yi aikin sarrafa karfe ba kama daga Kudanci har Arewacin kasar.

Ga dukkanin mai son ayimasa aikin sarrafa karfe zai iya garzayowa kamfanin Afuwa Welding Works ko kuma ya tuntubi kamfanin ta hanyoyin sada zumunta.

Share Articles:

Leave a Reply