Contact Info

Mukan Ziyarci Sassan Jihoshi Domin Yin Ayyuka Nagani Nafada.

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction suna ci gaba da sharafinsu wajen yin ayyuka masu nagarta da inganci kuma na gani na fada.

Domin kuwa wannan kamfani ya ciri tuta wajen yin kwangilar ayyuka da ake kiransu da mahadi ka ture wajen yadda ake jajircewa domin ganin komai an saka mai inganci.

Wannan baya rasa nasaba da jakircewar shugaban kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Eng. Mustapha Abdullahi Sani inda yake zuwa komai ayi a gabansa domin kuwa su wannan kamfani basa kwange ko coge.

Wannan kamfani na yin jigilar ayyukan karfe zuwa sassan jihoshin Najeriya har guda 36 da ake dasu kamar yadda kuke ganin motoci dauke da manyan karafuna.

Wannan kamfani ya kafa tarihin yin manyan ayyuka a Najeriya a kama daga manyan ma’aikatu da manyan guraren tarihi da dai sauransu.

Share Articles:

Leave a Reply