Yiwa karfe ado gami da kwalliya shine alkibilar kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ako da yaushe.
Hakan ce ma ta sanya kamfanin yake da manyan injinan sarrafa karfe kala-kala a lungu da sako na cikin kamfanin domin yiwa karfe ado wajen yimasa lankwasa.
Wannan kamfani dai ya kasance yana da ruwa da tsaki akan ko wanne irin karfe ta hanyar yimasa dukkanin aikin da ake da bukata kuma aiki mai nagarta da inganci.
Wannan kamfani ya dade yana sharewa kwastomonin sa hawaye wajen yimusu ayyuka irin wanda suke so kuma masu tafiya dai-dai da zamani tamkar daga kasar China.
Kalli yadda aka lankwasa sauran wadannan karafunan kuma lankwasa kala-kala tare da injinan lankwasar karfe a wannan kamfani.
Zaku iya bibiyarmu a shafukanmu na sada zumunta kamar facebook da tiktok da Instagram da YouTube da X da sauransu ko kuma a shafinmu na yanar gizo wato www.afuwaweldingworks.com




