Contact Info

Ayyukan Kujerun Karfe na Zamani Kala-Kala a Kamfanin Afuwa Welding Works.

Daga Amina Abdurrahman Hassan.

Karfe ya zamo ruwa da tsaki kuma jigo a dukkanin wani abu da ake gudanar wa wajen dorewar ingancin abin gami da nagarta.

Domin koanyan gine gine da ake kallo ko wannen su an sanya karfe a tsakiyar sa hakan tasa ya ke zaune daram ko motsi baya yi ballantana ace ya rushe.

Haka ma tuni duniya ta sauya wajen yin kujerun karfe, shiyasa kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction yake ayyukan kujerun karfe yana gudanar Ingantattu masu launi daban daban.

Kamfanin ya kasance yana karbar kwangilar ayyukan kujerun karafuna a kamfanoni da makarantu da masana’antu a fadin kasar Najeriya.

Bugu da kari yana yin kujerun karfe na zama a ofisoshi iri daban daban da suke tafiya da salon zamani ba tare da sun lalace ba inda wasu ake zuba su a falo da sauran lunguna da sako na cikin gida

A duk inda kuke a fadin duniya zaku iya turo da sakon ayyukan ku da ya shafi karfe ba iya aikin kujeru ba harma da sauran ayyukan da suka danganci karfe, kamfanin ya shirya sharemuku hawaye.

Share Articles:

Leave a Reply