Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance yana sharafi wajen sarrafa karfe ko wanne iri ne.
Haka wannan kamfani ya kasance yana gudanar da aiki ga wasu kasashe daga sassan duniya inda wasu suke zuwa har kamfanin domin ganewa idanunsu.
Daga ko wacce nahiya kuke daga cikin nahiyoyi 7 da muke dasu a duniya wato Afrika da Turai da Asia da Latin America wato kudancin Amurka da arewacin Amurka da Oshenia har ma da yankin Antactica za ku iya bibiyar shafukan mu na sada zumunta domin ganewa idonku irin ayyukan wannan kamfani.
Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance yana kirkirar sababbin ayyuka da babu irinsu kuma ya aiwatar dasu cikin salon fasahar zamani a dukiyar sarrafa karfe.
Haka zalika kamfanin ya kasance yana gudanar da ayyuka kala-kala da adadinsu ba zai lissafu ba kuma ayyuka masu nagarta gami da inganci.




