Daga Amina Abdurrahman Hassan.
Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works ya samu karbuwa, kuma yayi fintikau a kasar Najeriya dama kasashen makotan kasashe ta fannin sarrafa karfe.
Hakan baya rasa nasaba da kakkarfar alakar kamfanin da ita kanta kasar ta China baya rasa nasaba da jakircewar shugaban kamfanin kuma fasihi wajen kirkira da salon fasahar zamani wato Eng. Mustapha A Sani.
Tsabar bincike da kididdiga da kuma sanin aiki yasa yake kirkirar abubuwa da kayayyakin aiki tamkar irin yadda kasar China take kirkira, hakan yasa kasar ta so ya zauna a can wato China domin ci gaba da kirkire kirkirensa.
Shugaban ya kasance yana ketare manyan birane duk nisan su a kasar ta china don binciko kirkire kirkiren fasahohin zamani daban daban da zai inganta Kamfanin sa.
Daga cikin biranen da ya kaiwa ziyara sun hada da Beijing, Ghounzhou Shanghai, fuyang, Dazhou, Xiangyang, Suzhou, Yichun, Wuhan, da sauran su.
Da wannan yawon binciken ne Mustapha A sani ya Kara samin ilimi mai tarin yawa kan yadda ake sarrafa karafuna cikin launuka daban daban na fasahar zamani harma da injinan kera kere a kamfanin nasa.
Kazalika kamfanin ya kware wajen ayyukan sarrafa karfe ko wanne iri ne a fadin duniyar nan, kuma yana karbar aiki a sassa daban daban na fadin kasar nan dama kasashen ketare.




