Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance kamfani mai yiwa karfe yadda yaga dama wajen sarrafa shi.
Kamfani ne da yake da manyan injinan lankwasa karfe da yimasa ado ko wanne iri ne kuma komai kaurinsa da sirantakar sa kuma ko wanne kalar karfe ne.
Kamfani ne mai sauya salon aiki ako da yaushe kuma kamfanin yana da ma’aikata masu aiki da baaira gami da lirkire-kirkire na sababbin ayyuka.
Wadannan hotuna da kuke gani suna daga cikin ayyukan lankwasar da kamfanin ya gudanar tun a shekarun baya inda aka lankwasa wadannan karafuna cikin hikima da kwarewa.
Mamallakin wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Eng. Mustapha A Sani na yawan fadar maganar cewa wannan kamfani nasa yana da ruwa da tsaki akan ko wanne irin karfe.




