Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kasance yana gudanar da ayyukan rumfar karfe.
Rumfar ta kasance ta yin parking din motoci ko ta ajiye kayayyaki ko ta ajiyar dukkanin wani abu da ba a son ruwa ya taba shi da dai sauransu.
Kamar yadda ake kallon wannan sabuwar rumfar mai hade da fitila mai aiki da hasken rana da ake kira da Turanci (Solar) kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ne ya yi ta.
Wannan rumfa ta kasance mai inganci da nagarta gami da kwari sosai wadda ake kiranta da mahadi ka ture.
Irin wannan aikin wannan kamfani ya gudanar dashi a gurare da dama kuma dukkanin wanda aka yiwa irin wannan aikin yana nan yana ci gaba da cin gajiyar abinsa.




