Contact Info

Jerin Ayyukan Jami’ar North West Da Kamfanin Afuwa Welding Works Ya Gudanar.

Daga Amina Abdurrahman Hassan.

Ko kunsan cewa akwai kamfanonuwa da makarantu da kuma sauran manyan gine-gine da ake samun akasi wajen yimusu ingattaciyar raftar karfe ko sanya karfe da ya zama wajibi idan ana son su yi inganci da nagarta? Kamar yadda wasu suke kuka da kwangilar da suka bayar.

Ina masu kokawa kan cewa gine-gine na kwangilar da suka bayar ya ruguje, to albishirin ku, domin kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya saba sharewa al’umma hawaye wajen yimusu raftar karfe mai nagarta da inganci.

Wannan kamfani ya sha yin ayyukan raftar karfe a jami’o’i da dama kama daga jami’ar jihar Sokoto da kwalejin fasaha ta Adamu Husaini dake Kazaure a jihar Jigawa da makarantar Sa’adatu Rimi dake Kano har da jami’ar Bayero dake Kano da sauran manyan jami’o’i a kasar Najeriya.

Kamfanin bai tsaya iya nan ba domin kuwa suna gudanar da raftar karfe a manyan gidaje da kuma manyan masana’antu a sassan jihoshin kasar Najeriya.

Mafiya yawan ayyukan ginin raftar karfen jami’ar Northwest dake jihar Kano kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ne ya gudanar da su.

Kama daga ajujuwa karatun dalibai da manyan dakunan taro da kuma dakin karatun dalibai na wannan jami’ar wato (Library).

Haka zalika idan magana ake ta ayyuka masu inganci da nagarta na raftar karfe kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya yi fice.

Domin kuwa ayyukan Kamfanin kai tsaye za a iya kiransa da mahadi ka ture domin ingancin sa da kwarinsa ba a cewa komai.

Share Articles:

Leave a Reply