Kamar yadda aka sani kuma ake gani a kasa kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction kamfani ne da ya kware wajen yin ayyuka da ba za su lissafu ba sakamakon kullum kamfanin a fannin kirkirar sababbin ayyuka aka gina shi.
Daga cikin ayyukan da wannan kamfani ya ke gudanarwa har da aikin hada tankin ruwa kala-kala.
Ayyukan tankunan ruwa wannan kamfani ya gudanar da su a jihoshin Najeriya musamman ma a jihoshin Arewacin kasar.
Kamar yadda ake ganin wannan hoton na cikin labarin nan ma’aikatan kamfanin ne a lokacin da suke tsaka da aikin hada tankin ruwa a guda daga cikin jihoshin kasar ta Najeriya.
Shi wannan aikin na tankin ruwa ana yin sa a samfuri da dama wato kala-kala sai wanda mutum yake da bukatar ayimasa.




