Contact Info

Yadda Bayanan Shahararren Injin Point Welding Yake Ayyukansa.

Injin da ake kira da Point Welding yana daga daga cikin manyan injinan kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Sannan inji ne da duk Arewacin kasar Najeriya babu irin sa, sannan inji ne da yazo da abubuwan mamaki idan ana gudanar da aiki da shi.

Inji ne da ake amfani da hannu da kuma kafa a lokacin da ake gudanar da aiki da shi, sannan kuma injin an yimasa kirar raina kama kaga gayya.

Ana amfani da wannan jinjin wajen yiwa kyaure ko kofa walda cikin sauri, kafin kace kwabo tuni an gama yin waldar.

Sannan ta kasance walda ce da idan aka yita to bata bambaruwa, gam-gam take kamawa a jikin karfen da aka manne.

Share Articles:

Leave a Reply