Contact Info

Kamfaninmu Na Yin Manyan Kofofi Ko Wanne Kala.

Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kware wajen kera manyan kofofi masu inganci da nagarta.

Kamar yadda ake ganin wannan babbar kofar (gate) an yita da karfe mai inganci wato mahadi ka ture, domin daga ganin wannan karfen jikin babbar kofar ba sai anyi cikakken bayani ba dangane da nagartar sa.

Sai dai wannan kamfani ba iya wannan kalar salon babbar kofar ya ke yi ba, yana yin salo kala-kala sai wadda kwastoma ko mai siya ya zaba domin kawata kofar gidan sa.

Sannan akwai manyan kofofi na ginin gidan sarauta da wannan kamfani na sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yake yiwa sarakuna.

Sannan ko wacce irin kofa ka kwatanta ko kuma kazo da zanen ta to babbu shakka za ayimaka fiye da yadda kake zato wajen kawatarwa gami da ado na zamani kuma cikin sabon salon fasahar zamani.

Share Articles:

Leave a Reply