Contact Info

Haduwar Malam Ibrahim Shekaru Da Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works.

Biyo bayan saukar shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Eng. Mustapha A Sani zuwa kasar Saudiyya a yammacin jiya litinin, sun hadu da tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanatan Kano ta tsakiya Malam Ibrahim Shekarau.

Sun hadu ne  bayan isar su a kasar mai tsarki don gudanar da ibadar Umara a wannan wata mai albarka na Ramadan.

Idan za a iya tunawa a wasu kwanaki da suka gabata shugaban kamfanin Injiniya Mustapha Abdullahi ya kai masa ziyarar ta aziyya bisa rasuwa dan uwansa a gidansa dake nan jihar Kano.

Mustapha Abdullahi Sani dai ya kasance mutumin Shekarau tsawon shekaru masu yawa har kawo yanzu.

Ko a shekarun baya shekarau ya sha kawo ziyara lokuta da dama zuwa kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction inda wata rana har aka hango shi ya yi abin da ya saba na yin addu’o’i a dukkanin inda yaje.

Share Articles:

Leave a Reply