Contact Info

Bayanan Yadda Ma’aikatan Kamfanin Afuwa Welding Works Suke Hada Tubalin Ruwa.

Daga Amina Abdurrahman Hassan.

Tubalin ruwa ko madatsar ruwa wani abu ne da ake amfani da karfe wajen hada shi domin sanya shi a manyan magudanan ruwa da suka hadar da dam ko rafi ko korama ko babban gulbi ko kuma a ma aikatar ruwa (Water Board).

Shi tubalin karfe na ruwa yana taimakawa wajen hana ambaliyar ruwa zuwa hanyoyi ko kuma cikin gari wanda hakan ke janyo rushewar gari har ma da rasa rayuka.

Kamar yadda ake gani ga ma’aikatan Kamfanin sarrafa karafuna na Afuwa Welding Works And General Metal Construction suna kokarin yin ayyukan yanka wasu bangare na jikin tubalin ruwa a matakin farko.

Sannan a mataki na biyu Suna sarrafa karfe ta hanya fitar da Zane a jikin sa don su fitar da siffa tare da inganta shi wato a takaice ayyukan da ake kira mahadi ka ture.

Suna hada karafuna daban daban masu kwari wajen domin a samu ingantaccen tubalin da zai hana ballewar ruwa ko ambaliya.

Kamar yadda taken wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yake wato ayyuka cikin sabon salon fasahar zamani kuma kala-kala masu nagarta da inganci Ako da yaushe.

A matakin na uku ma za a ga ma’aikatan sun kammala hada tubalin, kuma ana iya amfani dashi a kowanne irin manyan dam ko rafi da sauran magudanan ruwa a ko ina.

Akwai tubalin magudanan ruwa kala-kala da ake hada su a kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works da ake amfani dasu ako ina a fadin tarayyar Najeriya.

Babban misali ga wani kalar nan na daban da aka kammala shi a wani lokaci da ya shude a baya inda ya bambanta da sauran wadanda ba a kammala su ba.

Share Articles:

Leave a Reply