Contact Info

Alakar Kamfanin Afuwa Welding Works Da Kwastomomi Naci Gaba Da Yaduwa Sabo Da Wasu Dalilai.

Daga Amina Abdurrahman Hassan.

Katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa welding Works And General Metal Construction yana gudanar da ayyuka daban daban ciki har da sababbin ayyukan da ake kirkirar su a nan take.

Kamfanin naci gaba da zuwarwa da kwastomomin sa sabon salon fasahar zamani domin yi musu aiki cikin inganci da nagarta akan farashi dai-dai da aljihun su.

Kamfanin anyi ittifakin babu tamkarsa a dukkanin fadin Arewacin kasar Najeriya, kuma kamfani ne da yake kyautatawa tare inganta alaka tsakanin sa da kwastamomin sa da ke sassan kasar da kuma kasashe daban daban a fadin duniya.

Inganci da sahihancin aikin kamfanin ne yake kara karfafa alakar su da kwastomomin su, duba da irin ayyukan da suke yi ba tare da ha’inci ba ko cin amana.

Kwastomomi da dama su kan ga ayyukan kamfanin ta hanyoyin daban daban kama daga masu zuwa kamfanin, da masu ganin samfurin ayyukan a wasu jihoshin, wasu mutanen kuma suna ganin ayyukan ta shafukan sada zumunta na zamani da shafin yanar gizo na kamfanin daga ko ina a fadin duniya.

Wannan kamfani na Afuwa Welding Works ya gudanar da ayyuka da dama da aka kaisu wasu kasahse kamar Indiya da Kamaru ds Chadi da Nijar da Senegal da sauran su.

Haka zalika wasu daga cikin kwastomomin kamfanin su kan turo da samfurin kalar ayyukan da suke so ba tare da sunzo ba kuma ayimusu shi fiye da yadda su kai tsammani.

Kamfanin yana gudanar da ayyuka kala-kala da hadar da kofofin zamani, rafter karfe, fitulun kan titi, tankuna ruwa, gina gidajen mai, tubalin ruwa da sauran ayyukan da suka danganci sarrafa karfe zuwa launuka da siffofi iri iri.

Sannan kuma kamar yadda shugaban kamfanin yake fada kuma yake sake nanatawa wato Injiniya Mustapha Abdullahi Sani,cewa har yanzu kamfanin bai sauya ko karin kudin aiki ba. Yadda ake biya a shekarun baya yanzu ma haka ake biya.

Share Articles:

Leave a Reply