Contact Info

Yadda Ma’aikatan kamfanin Afuwa Welding Works Suke Aiki da Binding Machine.

Kamar yadda duniya ta sani kuma take gani akwai injina mabambanta a kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Wadannan injina dai wasu an kawo su daga kasar China inda wasu kuma aka yi amfani da kwakwalwa gami da basira aka kera su a cikin kamfanin na Afuwa Welding Works.

Fasihin Injiniya wato Mustapha Abdullahi Sani kuma shine mamallakin wannan kamfani shine yake kirkirar su kuma ya kera su nan take su kama aiki tamkar daga can kasar China aka kawo su.

Wannan inji na lankwasar karfe ba iya mutum daya ne yake aiki da shi ba, mutane da yawa ne suke aiki da shi wajen yiwa karfe yadda aka ga dama. Ma’ana dai shi wannan injin ana amfani da karfi wajen lankwasa karfe.

Amma akwai injinan lankwasar karfen da kawai masarrafi (remote) ake amfani dashi wajen lankwasa karfe mutum yana daga gefe.

Wannan inji dai yana yin ayyuka kala-kala kuma dai-dai da zamani wajen yin lankwasa irin wadda kwastoma ya bayyana cewar yana so.

Wannan kamfani dai ya zamanto abin koyi ga sauran kamfanonin sarrafa karfe domin kusan ko wanne aiki idan ka gani akwai sabuwar kirkira gami da fasahar zamani wajen kera ko wanne karfe.

Share Articles:

Leave a Reply