Kwastomomi daga sassa daban-daban naci gaba da yabo gami da jinjinawa kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.
Wannan yabo ya biyo bayan yadda kamfanin ya ke ci gaba da yin ayyuka masu nagarta da inganci a sassan kasar Najeriya harma da makotan kasashen dake nahiyar Afrika wato kasashen Togo da Senegal da Cameroon da Chad da Niger da sauran su.
An kafa wannan kamfani na sarrafa karfe na Afuwa Welding Works tun a shekaru masu yawa da suka shude kuma kamfanin yana nan a kan bakar sa na yin ayyuka masu nagarta da inganci.
Kuma shi wannan kamfani a shirye yake da ya sharewa kwastomomi hawaye wajen yimusu kalar aikin da suke so.
Shi kansa mamallakin wannan kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Eng. Mustapha A Sani ya bayyana cewar kamfanin sa zai ci gaba da farantawa kwastomomin sa a ko ina suke a fadin duniya.




