Kamfani mai tafiya dai-dai da zamani a duniyar sarrafa karfe wato Afuwa Welding Works ya kware a fannoni da dama a ayyukan sarrafa karfe.
Domin kuwa a yanzu wannan kamfani ayyukan da yake gudanarwa ba za su iya lissafuwa ba kamar yadda shugaban kamfanin yake fada ako da yaushe wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani.
Sannan wani abin mamaki wanna kamfani ako da yaushe ya kan kirkiro sababbin ayyuka na sarrafa karfe da ake fara yinsu a nan take a wannan kamfani.
A wannan gabar za muyi bayani a kan ayyukan raftar karfe da wannan kamfani yake gudanarwa a sassan jihoshin Najeriya.
Ita kanta raftar karfen wannan kamfani yana gudanar da ita kala daban-daban kamar yadda ake gani a hotunan cikin labarin nan da muke bayarwa a shafin yanar gizo na wannan kamfani.
A kasar mu ta Najeriya akwai jihoshin Arewa maso Yamma da su ka hadar da Kano da Katsina da Sokoto da Kebbi da Zamfara da Kaduna da Katsina da kuma Jigawa, dukkanin jihoshin nan babu inda kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction baije ya yi ayyukan raftar karfe ba.
Haka zalika a jihoshin Arewa maso Gabas ma da su ka hadar Bauchi da da Gombe da Yobe da Maiduguri da Taraba da Adamawa. Dukkanin wadannan jihoshi babu inda kamfanin Afuwa Welding Works baije ya yi ayyukan raftar karfe ba.
Sannan a jihoshin Najeriya ta tsakiya wato Niger da Jos da Benue da Kogi da Kwara da uwa uba babban birnin tarayya Abuja (FCT) babu inda kamfanin Afuwa Welding Works baije ya yi ayyukan raftar karfe ba.
Haka zalika a jihoshin Kudu maso Kudu wato bangaren kabilar Yarawa (Yoruba) kamfanin Afuwa Welding Works yayi ayyukan raftar karfe a wasu daga cikin jihoshi, musamman jihar Lagos akwai ayyukan wannan kamfani.
Sannan bangaren Kudu maso Gabas wato bangaren kabilar Inyamurai (Igbo) wannan kamfani ba a barshi a baya ba yaje ya yi ayyuka.
Biyo bayan irin wannan ayyukan raftar karfe masu inganci da nagarta wannan kamfani ya ciri tuta wajen yin aiki mahadi ka ture.




