Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya kawata jami’ar nan dake karamar hukumar Sumaila da ado na kawatawa a jikin karfe wanda aka yi ado dasu a sassan makarantar.
Kamfanin dai kamar yadda aka sani ya saba bijiro da ayyuka gami da kirkira cikin sabon salon fasahar zamani ta hanyar amfani da injina na zamani na sarrafa karfe.
Inda aka yi amfani da injin CNC Plasma Cutting Machine wajen yin wannan kawataccen ado na kasaita da aka sanya a wannan jami’a ta AUSU.
Cikakken sunan jami’ar shine Al-Istiqama University Sumaila, Kano. Kuma jami’a ce da take da gogaggun malamai da hazikan dalibai.
Kamar yadda ake gani shi kansa karfen wajen yimasa ado an yi amfani da wancan suna wato AUSU a jikinsa.
Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction na maraba da kwastomin sa daga ko ina suke a sassan dukiya domin kulla alaqar yimusu aiki mai nagarta da inganci.




