Bayanan Wasu Samfurin Kyamaran da Ake Buga su a Kamfanin Afuwa Welding Works.
Kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya saba buga kyamara ko kofofi na gani na fada kuma na alfarma.
A shekarun baya kamfanin ya kasance yana yin kofofi da hannu amma kuma a yanzu haka inji ne yake buga kyamaran cikin kankanin lokaci.
Akwai mauli kala-kala a kamfanin wanda da zarar kwastoma ya zo ya nuna kalar da yake bukata to babu makawa za a yimasa ko kofofi guda nawa yake so.
Domin kuwa akwai injin buga kyamara sukutum guda da yake a kamfanin na Afuwa Welding Works wanda ya kan iya buga kofofi sama da 1000 a rana daya.
1.
2.
Wadannan da ku ka gani samfur ne kamar yadda suke a tsaitsaye kuma masu nagarta da inganci.
Kuci gaba da bibiyar shafin yanar gizo na kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction domin sanin abubuwan dake faruwa na ayyuka kala daban-daban a kamfanin.