Contact Info

Zunzurutun Bayanai Dangane da Rafta ta Karfe (Metal Rafters) da Kamfanin Afuwa Welding Works Yake Gudanarwa a Sassan Kasar Najeriya.

Katafaren kamfanin sarrafa karfe kuma kamfanin da babu tamkarsa a Arewacin kasar Najeriya ya kasance yana gudanar da ayyukan rafta ta karfe ta musamman kuma mai nagarta da inganci.

Hakan ce ma ta sanya kusan a dukkanin jihoshin kasar Najeriya guda 36 kamfanin yake yin ayyuka kala-kala, kama tun daga rafta ta karfe zuwa wasu ayyukan.

Kamar yadda ake ganin wadannan hotunan na wannan rafta ta karfe, kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ne ya gudanar da su a sassa kasar nan ta Najeriya.

Kuma dukkanin kamfani ko ma’ajiya ko gidan mai da sauran masana’antun da kamfanin Afuwa Welding Works ya yimusu aiki tabbas suna yabawa da ingancinsa.

Hakan ta sanya wannan kamfani ya ciri tuta wajen yin aikin rafta ta karfe da sauran ayyukan da yake yi a cikin kamfani da wajen kamfani.

Kamfaninmu na yin aiki a kowacce jiha a kasar nan, kuma kasashen waje suna shigowa domin kawowa wannan kamfani aiki kamar Senegal da Cameroon da Togo da Mali da Niger da Chad da sauransu.

Send:

Leave a Reply