Contact Info

Yusuf Maitama Sule University: Yadda Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction Yayimana Ayyuka Masu Nagarta

Jami’ar Yusuf Maitama Sule naci gaba da jinjinawa katafaren kamfanin sarrafa ƙarfe da babu kamarsa a Arewacin Najeriya wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Badon komai ba sai don yadda wannan kamfani ya gudanar da ayyukansa masu inganci da nagarta a wannan jami’ar a lokacin da ake tsaka da gina makarantar.

Kamfanin na Afuwa Welding dai shine ya gudanar da ayykan rafta ta ƙarfe a kusan kowacce tsangaya ta makarantar kuma aiki mai nagarta sosai da sosai.

Wannan makaranta wadda da farko aka sanyamata suna North West University sannan aka sauyamata suna zuwa Yusuf Maitama Sule University an kafata a shekarar 2012 a lokacin mulkin Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.

Wannan makaranta dai a lokacin da aka kafa ta tana da Faculty sama da 12 sannan kuma tana da department (Tsangaya) 71, haka zalika tana da programs guda 267.

Ga jerin Faculties ɗin da Jami’ar Yusuf Maitama Sule take dasu kuma a kusan kowanne Facility kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya yi raftar ƙarfe.

1. Faculty of Agriculture.

2. Faculty of Basic Medical Sciences

3. Faculty of Clinical Sciences

4. Faculty of Education

5. Faculty of Engineering

6. Faculty of Environmental Sciences

7. Faculty of Humanities

8. Faculty of Information and Communication Technology

9. Faculty of Law.

10. Faculty of Pharmaceutical Sciences

11. Faculty of Science

12. School of General, Entrepreneurial and Remedial Studies

13. School of Postgraduate Studies

14. Centre for Continuing Education (CCE).

Kamar yadda ake gani sabo da tsabar ƙwarewar kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato kamfanin Alhaji Mustapha A Sani aka baiwa kwangilar raftocin ƙarfen (Metal Rafters) kuma ya kammalasu cikin nasara.

Wajen gabatar da aikin kamfanin ya nuna ƙwarewa wajen saƙa ƙarafunan ta yadda komai ya tafi dai-dai kuma haryanzu gine-ginen tamkar ƙaramasa ƙwari akeyi.

Wannan kamfani yana gudanar da ayyukansa a sassa daban-daban na ƙasar nan kuma a jihohin Kudu da Arewa.

Send:

Leave a Reply