Contact Info

Yadda Manajan Bankin First Bank da Jama’arsa Suka Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works Wato Lunguna da Sako Domin Ganewa Idonsu.

Yadda Manajan Bankin First Bank da Jama’arsa Suka Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works Wato Lunguna da Sako Domin Ganewa Idonsu.

 

Manajan bankin First Bank reshen Kofar Ruwa da tawagarsa sun ziyarci katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Sun ziyarci kamfanin a ranar Talata 15 ga watan May, 2024 inda suka sami tattaunawa da shugaban wannan kamfani wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani.

Kafin wannan ziyara tasu daman akwai kyakyawar alaka tsakanin wannan banki da kuma wannan kamfani.

Yayin ziyarar tasu shugaban wannan kamfani ya zagaya dasu lungu da sako gami da kowanne sashen wannan kamfani.

Kama daga sashen na’ura mai kwakwalwa (computer) da sashen injinan buga kyamara (door printing) da sashen injinan karkatar da karfe (binding) da sashen walda da sashen huda karfe da sauran ko wanne sashe.

Haka zalika Engineer Mustapha Abdullahi Sani ya yimusu bayanai akan ko wanne inji dangane da yadda yake gudanar da aikinsa da muma gwadamusu komai da komai.

Daga karshe sun yabawa wannan kamfani tare da dukkanin ma’aikatan kamfanin bisa jajircewar da sukeyi wajen habbako da Arewacin kasar Najeriya da irin wannan fasaha ta sarrafa karfe.

Send:

Leave a Reply