Contact Info

Yadda Kamfanin Afuwa Welding ya Bayar da Gudun Mawa Wajen Gina Dam Ɗin Obajana Ashekarun Baya.

Magudanar ruwa ko Dam ɗin Obajana Dam ne mai cikakken tarihi wanda ya kwashe shekara da shekaru, domin kuwa a lokacin da za’a fara yin Siminti na kamfanin Ɗangote da ake kira da Ɗangote Cement anyiwa Dam ɗin aiki na musamman.

A lokacin da aka dinga amfani da pipe ɗin ƙarfe wato joint na gina Dam dake Obajana kamfanin Afuwa Welding ya bayar da gudun mawa wajen ƙera pipe ɗin da akayi amfani dashi wajen gina magudanar ruwa.

Domin kuwa kusan dukkanin wani joint da aka gina wannan Dam to Alhaji Mustapha A Sani mamallakin katafaren kamfanin sarrafa ƙarfe da ake kira da Afuwa Welding Works And General Metal Construction ne yayi wannan ayyuka kuma dashi akayi aikin.

Garin Obajana dai ya kasance a jihar Kogi wadda take a Najeriya, kuma garin yana ƙarƙashin Ƙaramar Hukumar Oworo.

A wannan Ƙaramar Hukumar katafaten Kamfanin Simintinnan na shahararren attajirinnan Alhaji Aliko Ɗangote yake.

Biyo bayan aikin saka ƙarfen magudanar ruwa mai inganci ake da buƙata shine aka baiwa Alhaji Mustapha Afuwa kwangilar yin aikin kuma kamfanin na Afuwa Welding Works And General Construction ya kammalashi cikin nasara.

Alhaji Mustpha A Sani shine yake bayar da labarin lokacin musamman a wasu ayyuka da yake tunawa kuma yake bayar da labarin irin gwagwarmayar da yasha wajen gudanar dasu a jihohi daban-daban na Najeriya.

“A lokacin da mukayi wannan aikin na Obajana munyishine tare da Eng. Mustapha da kuma marigayi Eng. Tijjani, Allah jiƙansa ya gafartamasa”.

Send:

Leave a Reply