Contact Info

Yadda Kamfanin Afuwa Welding Works & General Metal Construction ya Gudanar da Aikin Raftar Ƙarfe a Kwalejin Fasaha ta Hussaini Adamu Kazaure

Makarantar Kwalejin Fasaha da ake kiranta Husaini Adamu Kazaure tana daga cikin wuraren da katafaren kamfanin sarrafa ƙarfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar da ayyuka masu nagarta da inganci.

Wannan kamfani dai ya ƙware wajen yin ayyuka a sassa daban-daban na ƙasar nan ta Najeriya daga Kudanci har zuwa Arewacin ƙasar.

Dukkanin rafta ta ƙarfe (Metal Rafters) da aka gudanar lokacin da ake gina makarantar Kwalejin Fasaha ta Husaini Adamu Kazaure kamfanin Afuwa Welding Works ne ya gudanar da ita.

Wannan makaranta dai an ƙirƙireta a shekarar 1991 domin ci gaba da bunƙasa ilimi a Najeriya musamman ta fannin fasaha da tsumi da tanadi.

An sauyawa makarantar suna a shekarar 1998 domin nuna girmamawa da kuma tunawa da marigayi sarkin Kazaure Alhaji Husaini Adamu.

Wannan makaranta ta zamo Kwalejin Fasaha a watan Janairu na shekarar 2007.

Sakamakon ayyukan da katafaren kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar a kamfamin ya sanya har yanzu tamkar sabon aiki ne biyo bayan yadda kamfanin ya ƙware wajen ayyuka masu nagarta.

Wannan makaranta tayi bikin yaye ɗalibai karon farko a watan Feburairu na shekarar 2009 inda ta yaye ɗalibai 6,024 waɗanda suka kammala karatu daga shekarar 1992 zuwa 2008.

Ga jerin kwasa-kwasan da wannan makaranta take koyarwa kamar haka:

1. Accountancy

2. Agricultural Technology.

3. Architectural Technology.

4. Building Technology.

5. Business Administration & Management.

6. Civil Engineering Technology.

7. Computer Engineering.

8. Computer Science.

9. Electrical /Electronic Engineering.

10. Estate Management & Valuation.

11. fashion Design & Clothing Technology.

12. Forestry Technology.

13. Library And Information Science.

14. Mass Communication.

15. Mechanical Engineering Technology.

16. Mechatronics Engineering Technology.

17. Office Technology And Management.

18. Polymer Technology.

19. Printing Technology.

20. Quantity Surveying.

21. Science Laboratory Technology.

22. Urban & Regional Planning.

23. Statistics.

Biyo bayan irin ayyukan da wannan katafaren kamfanin ya gudanar a sassa daban-daban na ƙasar nan da kayayyakin ayyuka na zamani da aka kawo zuwa kamfanin da kuma ayyuka na zamani da ake gudanarwa to wannan kamfani ya zama gagarabadau kuma babu tamkarsa a Arewacin Najeriya.

Send:

Leave a Reply