Contact Info

Yadda Eng. Mustapha A Sani ya Sauka a birnin Cairo Daga Nan Kuma ya Sake Tashi Zuwa Birnin Ghounzou Dake Kasar China.

Yadda Eng. Mustapha A Sani ya Sauka a birnin Cairo Daga Nan Kuma ya Sake Tashi Zuwa Birnin Ghounzou Dake Kasar China.

 

Yadda Eng. Mustapha A Sani ya Sauka a birnin Cairo Daga Nan Kuma ya Sake Tashi Zuwa Ghounzou Dake Kasar China.

A jiya Talata shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Engineer Mustapha Abdullahi Sani ya sauka a birnin Cairo dake kasar Masar (Egypt).

Alhaji Mustapha dai ya tashi daga daga Najeriya ta filin sauka da tashi na Malam Aminu Kano dake a jihar ta Kano inda jirgin ya nufi Arewacin Afrika wato birnin Cairo.

Bayan sun sauka a birnin na Cairo su kayi hutun wasu awanni kana daga bisani kuma su ka sake tashi zuwa can kasar China.

Wannan tafiya da yayi zuwa kasar ta China ba komai ne ya kaishi ba sai halartar bikin baja kolin da kaar China ta saba yi lokaci zuwa lokaci wato wani biki da suke baje hajojinsu.

Yayin tattaunawa dashi a daren Talata ta shafin WhatsApp Eng. Mustapha A Sani ya dauki hotunansa a lokacin da yake a birnin Cairo gabanin tafiyarsu Ghounzou dake kasar China.

Jigon wannan tafiya dai da shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works yayi, zai sake duba yadda zaici gaba da kara inganta kamfaninsa domin jin dadin kwastomominsu da kuma ci gaba da inganta ayyukan kamfanin.

Eng. Mustapha A Sani ya saba halartar wannan bikin bajakoli da kasar China take gudanarwa, sannan kuma ya saba zuwa kasar lokaci zuwa lokaci.

Send:

Leave a Reply