Contact Info

Yadda Eng. Mustapha A Sani ya Sake Inganta Injin da Yake Binding Din Karfe Wajen Sake Karamasa Karfi Sabo da…

Yadda Eng. Mustapha A Sani ya Sake Inganta Injin da Yake Binding Din Karfe Wajen Sake Karamasa Karfi Sabo da…

 

Shugaban kamfanin Afuwa Welding Works wato Engineer Mustapha A ya sake inganta wani bangare na jikin katafaren injinnan da yake lankwasa karfe koma wanne iri ne.

Ya sake inganta shi ne ta hanyar karamasa karfi wajen sake sakamasa wasu abubuwa gami da yimasa walda mai karfi a wasu sassa nasa.

Kamar yadda ake kallon shugaban wannan kamfani a cikin kayan aiki ga shi nan a lokacin da yake gudanar da wannan aiki na musamman.

Wannan aiki dai ya gudanar dashi cikin salo na musamman wajen ganin cewa ya yiwa wannan inji nagartaccen aiki da zaici gaba da bayar da abin da ake so.

Idan za a iya tunawa kuma kamar yadda ake gani a ko yaushe akwai manyan injina a wannan kamfani, kuma a watan da ya gabata na Satumba (September) aka hamgo Engineer Mustapha Abdullahi Sani yana sake inganta injinnan da ake amfani dashi wajen buga kyamara inda shima aka sake inganta shi.

Allah ya baiwa Engeneer Mustapha A Sani basira da kaifin kwakwalwa wajen yin dukkanin mai yiwwuwa domin gyaran injinan kamfaninsa da sauran yiwa karfe salo wajen yin aikin da babu irinsa.

Kuci gaba da bibiyar shafinmu na yanar gizo na wannan kamfani wato www.afuwaweldingworks.com domin ci gaba da kallon ayyuka kala daban-daban a suniyar kere kere cikin sabon salon fasahar zamani.

Send:

Leave a Reply