Contact Info

Yadda Eng. Mustapha A Sani Ya Kara Inganta Injin Dake Buga Kwamara da ya Kawo Shi Daga Kasar China a Kamfaninsa na Afuwa Welding.

Daga Amina Abdurrahman.

Tabbas kowa ya san matukar aka ambaci sunan kasar China a duniyar kere-kere to an gama magana biyo bayan sun shiga gaban kowacce kasa a duniyar kere-kere.

Kamar yadda shahararren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works ya saba zuwa kasar China domin kawomuku injinan sarrafa karfe dai-dai da zamani.

Haka shugaban wannan kamfani Allah Ya horemasa basirar kera wasu injinan da hannunsa a Kamfaninsa dake jihar Kano a tarayyar Najeriya.

Wannan inji da kuke gani Engineer Mustapha A shine ya kawo shi zuwa Kamfaninsa na Afuwa Welding Works a shekarun baya.

Biyo bayan kullum ana aiki dashi shine ya sake duba abin da bashi da inganci sosai a jikinsa domin sanya mai kwari da inganci biyo bayan yadda wani abin a jikin injin bai kai kwari da ingancin da ake da bukata ba.

Akwai wani karfe a can kasan injin da yake a gaba da baya, shine Engineer Mustapha A Sani ya nunawa kwararrun ma’aikatansa su cire karfe da aka sanya daga kasar China domin saka wani wanda ya fishi inganci da nagarta da ba zai sake lalacewa da wuri ba.

Kamar yadda ake ganin tartsatsin wuta na tashi tana feshi a lokacin da ake gyaran wannan inji.

Irin wadannan salo kala-kala na kirkira domin yiwa kwastomomi aiki mai nagarta da inganci ya sanya kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya yi fice gami da kere sa’a a Kano da Najeriya dama Afrika baki daya.

Yadda Eng. Mustapha A Sani Ya Kara Inganta Injin Dake Buga Kwamara da ya Kawo Shi Daga Kasar China a Kamfaninsa na Afuwa Welding.

Send:

Leave a Reply