Contact Info

Yadda Aka Fara Kammala Samfurin Sabuwar Fasahar da Eng. Mustapha A Sani ya Kirkira Dangane da Kyamara ko Kofofi a Wannan Shekarar.

A yanzu haka an fara kammala kyamare da aka ga shafukan wannan kamfani na sada zumunta ya fara kammaluwa wato abin yin zane ko gurbi da Eng. Mustapha A Sani ya kirkira.

Idan za a iya tunawa a kwanakin baya an ga wasu kyamara kamar yadda kuke ganinsu gayansu da ramuka na ado a jikinsu.

Wannan sabuwar kirkirar ko muce abin da Eng. Mustapha A Sani ya kirkira zai iya yin kyamare guda 100 a rana daya.

Haka zalika wannan hoton kuayren na biyu da muka saka lokacin da ake kan hanyar kammala kyauren kenan.

Idan ba a manta ba Eng. Mustapha A Sani ya kasance gwani ne ta fannin kirkire-kirkire domin ya kirkiri abubuwa da dama wanda har ta kasance kasar China ma tana amfani da fasaharsa da ya kirkira dangane da wani inji tun a shekarun baya.

A yanzu haka wannan kamfani ya kasance babu tamkarsa a dukkkanin Arewacin Najeriya musamman wajen fannin kirkira da ayyuka masu nagarta.

Haka zalika a fadin tarayyar Najeriya ana alfahari da shugaban wannan kamfani Alhaji Mustapha A Sani wajen samarwa da matasa aikin yi.

Sannan kuma wannan hoton na 3 da muka sanyamuku na wannan kofar ko kyaure lokacin da aka yiwa wannan kyaure fyanti ne wato aka kammala shi, inda aka yimasa farin fyanti.

Haka zalika nan gaba za ayi launching na wannan sabuwar kirkira a fannin bidiyo da kuma a rubuce, kuma za a ga yadda aka kammala yimusu fyenti su ka zamo kammalallu.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani ya bayyana cewar za a dinga ganin zane kala-kala ko wadannan gurabe a jikin kyaure masu bayar da sha’awa kuma masu nagarta.

Send:

Leave a Reply