Contact Info

Yadda Aka Fara Aiki da Sababbin Maulin Buga Kyamara Rigis da Aka yo Odarsu Daga Kasar China a Kamfanin Afuwa Welding Works

Yadda Aka Fara Aiki da Sababbin Maulin Buga Kyamara Rigis da Aka yo Odarsu Daga Kasar China a Kamfanin Afuwa Welding Works

 

Kamar yadda kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya saba farantawa kwastomominsa kuma ya saba yo odar kayayyakin aiki na zamani daga kasar China.

Yanzu ma hakan ta sake faruwa biyo bayan yadda kamfanin ya sake kawo sababbin mauli na buga kyamara daga kasar China.

Akwai sauran mauli da yawa kuma ko wanne da kalar zanen da yake fitarwa idan za a buga kofa a wannan katafaren kamfani.

Amma yanzu an sake kawo sababbi kuma na musamman masu fitar da sabon zane guda hudu (4) rigis kamar yadda ake kallon samfurin zanen da suka fitar kamar yadda ake gani.

Wannan inji dai da ake amfani dashi na buga kofofi ko kyamara a rana daya akan fitar da sama da guda Dubu Daya (1000).

Idan ba a manta ba shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Engineer Mustapha Abdullahi Sani kwanannan ya dawo daga kasar China inda ya halacci bikin baja kolin da aka gudanar a birnin Ghounzou.

Zuwansa can din ya kara yin bincike domin ganin nan gaba me ya kamata ya sake kawowa kamfaninsa domin ci gaba da tafiyar da ayyukansa cikin zamanantarwa.

Wannan shi ake kira da gani ya kori ji a kamfanin Afuwa Welding Works domin dukkanin mutumin da ya shigo kamfanin zata zaiyi a kasar China yake idan yaga ana yiwa karfe yadda aka ga dama.

Yanzu dai ga dukkanin mutumin da yakeson a bugamasa kofofi na musamman kai tsaye zai iya garzayowa kamfanin Afuwa Welding Works daga sassan Najeriya dama sauran kasashe.

Send:

Leave a Reply