Contact Info

Ya Kamata Wasu Daga Cikin Al’ummar Musulmi su Daina Yin Rantsuwa Akan Karya – Alhaji Mustapha A Sani.

Shugaban katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Alhaji Mustapha A Sani ya yi jan hankali akan wasu daga cikin ‘yan uwa Musulmi.

Yayi wannan jan hankalinne a tsarabar goron Juma’a da ya saba yi a kusan kowanne mako.

Yayi wannan jan hankalin akan yadda wasu a matsayimsu na Musulmai suke yin rantsuwa akan karya.

“Ina kira da nusarwa da kuma nasiha ga wasu daga cikin ‘yan uwa Musulmai akan yin rantsuwa akan karya da suke yi kuma alhalin sun san karya sukeyi, to ya kamata ku sani cewa Kaffara tana hawa kan mutum kuma wasu sun san hakan wasu kuma suna da karancin sani akan hakan. Ya kamata masu yi su daina”.

Alhaji Mustapha A Sani ya kara da cewa ko da mutum yana da gaskiya ba ko yaushe akeson mutum ya dinga yin rantsuwa ba.

Daga karshe mamallakin kamfanin na Afuwa Welding Works yayi addu’ar Allah ya bamu damuna mai albarka.

Send:

Leave a Reply