Contact Info

Wasu Muhimman Bayanai Dangane da Yadda Ake Lankwasa Karfe Yayin Tattaunawa da Managing Director na Kamfanin Afuwa Welding Works Alhaji Mustapha A Sani.

Batu akan lankwasa karfe komai girmansa kuma komai kaurinsa batu ne da yake yiwa mutane yawo a kwakwalwa musamman wajen yadda aka ambata cewar komai kaurimsa kuma komai girmansa.

Haka zalika da aka ambaci cewa ana yiwa karfe yadda aka ga dama a katafaren kamfanin sarrafa karfe da babu tamkarsa a Arewacin kasar Najeriya wato kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Wannan kamfani ya kware wajen lankwasa karge ko wanne iri ne biyo bayan yadda kamfanin yake da kayayyakin aiki na gani na fada.

A yayin tattaunawa da managing Director na wannan kamfani Alhaji Mustapha A Sani wanda ake kira da Mustapha Afuwa ya warware zare da abawa akan yadda lankwasa karfe take komai girmansa kuma komai kaurinsa.

“Tabbas mutane sukan yi mamaki idan suka ga yadda ake sarrafa karfe domin mayar dashi wata siffa ta ban, wasu mutanen sukan ziyarci kamfaninmu domin ganin yadda ake gudanar da ayyukan lankwasa karfe. Mukan auna karfe muga iya kaurinsa sannan muga wanne kalar inji zamuyi amfani dashi wajen yiwa kwastoma aiki mai nagarta cikin sabon salon fasahar zamani”.

Alhaji Mustapha A Sani bai tsaya iya nan ba yaci gaba da cewa.

“Dukkanin wasu masu walda idan wani aiki ya gagaresu na huda karfe ko aikin lankwasa karfe ko kuma aikin bankara karfe komai kaurinsa su kan zo kamfaninmu mu yimusu, sannan kuma suma kwastomomi sukan zo wannan kamfani daga sassan kasarnan mu yimusu aikin lankwasa karfe. Kuma ko yaushe muna maraba da dukkanin wanda za’ayiwa aikin lankwasa karfe yazo zamuyimasa”

Wannan kamfani da Afuwa Welding Works yana gudanar da ayyuka kala-kala sama da kala 50.

Haka zalika wannan kamfani a kullum cikin kitkirar sabon abu yake, wato kirkirar abin da babu irinsa.

Send:

Leave a Reply