Contact Info

Wasu Muhimman Bayanai Daga Kamfanin Sarrafa Ƙarfe Wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction

Kamar yadda akasani katafaren kamfanin sarrafa ƙarfe da dukkanin Arewacin Najeriya babu kamarsa wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction Company yana ta sakin muhimman abubuwa musamman a shafukan sada zumunta na kamfanin.

Biyo bayan zaman tattaunawa da Director General na wannan kamfani kuma mamallakin wannan kamfani Alhaji Mustapha A Sani ya yi da Babban Edita na shafin yanar gizo na kamfanin wato Suraj Na’iya Kududdufawa da kuma Eng. Bashir Aliyu Zubair wato wanda yake kula da sashen yanar gizo na kamfanin da kuma sauran ma’aikata na wannan sashe na yanar gizo harda shi kansa Mustapha A Sani.

A yayin tattaunawar dai Mustapha A Sani da Suraj Na’iya Kududdufawa da Eng. Bashir Aliyu Zubair sun zagaya sosai a kamfanin musamnan yadda Alhaji Mustapha A Sani ya fitar da bayanai akan sabon injin sarrafa ƙarfe da ya sake kawowa daga ƙasar China maisuna CNC Plasma Cutting Machine wato injin da yake fitar da kalar zane sama da guda 1000.

Mustapha A Sani dai ya bayyana cewar jama’a da dama na ganin CNC Machine da Lizer Cutting Machine duk ɗaya ne, amma kuma suna da bambanci, domin dukkanin aikin da CNC Machine zaiyi shima Lizer Cutting Machine zaiyi kawai bambancinsu shine finishing.

A yanzu akwai manyan injina a wannan kamfani da suke sarrafa ƙarfe kala-kala da suka haɗar da Door Printing Machine wato injin da zai iya yin ƙofofi sama da 1000 a rana ɗaya da Thick Plate Binding Machine da Metal Stamping Cutting Machine da Threading And Twisting Machine da Plate Cutting Machine da sauransu.

A yayin tattaunawa a tsakaninsu dangane da shafin yanar gizo na kamfanin nan gaba a hankali dukkanin ayyukan da wannan kamfani ya gudanar a kowacce jiha a Najeriya a shekarun baya to mutum zaije ya gansu kuma ya karanta labari dangane da aikin.

Biyo bayan yadda Mustapha A Sani ya gina wannan katafaren kamfani, kamfanin ya ginu sosai, su kansu mutanen ƙasar China idan suka kawomasa ziyara abin yana basu mamaki.

Domin ko da a makon da ya gabata saida wani mazaunin ƙasar China yazo yana neman inda za a yimasa aiki ya rasa, amma da aka turoshi wannan katafaren kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction abin ya bashi mamaki inda yace tabbas yadda yaga kayayyakin aiki tamkar a ƙasarsa ta China yake.

Daga ƙarshe dai Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) ya bayyana cewar dukkanin wanda yakeson a fitarmasa da wani zane (design) ki lanƙwasa ƙarfe dukkanin yadda yake to ba sai mutum yaje Lagos ko jihar Rivers ba, kawai yazo katafaren kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Zaku iya bibiyarmu a shafuka kamar haka.

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter: Afuwa Welding Works

Send:

Leave a Reply