Contact Info

Tunatarwa Gami da Goron Juma’a Awannan Rana ta Arfa – Alhaji Mustapha A Sani.

A wannan rana ta Juma’a mai albarka ake gudanar da hawan Arfa wato rana mafificiya a dukkanin ranakun mako.

Haka zalika a wannan rana al’umma da yawa suna yin azumin ranar Arfa da aka saba yinsa ako wacce shekara.

Mamallakin katafaren kamfanin sarrafa karfe na Arewacin Najeriya na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Alhaji Mustapha A Sani ya yiwa al’ummar Musulmi fatan alkhairi da kuma fatan dacewa da wannan falala ta wannan rana a wajen Allah S.W.A.

“Tabbas yin Azumi a wannan rana akwai lada mai yawa, sannan kuma an tambayi manzon Allah dangane da Azumin ranar Arfa sai yace, yin Azumi a wannan rana Allah yana gafartawa mutane kura-kurensu da suka wuce da kuma na wasu shekaru masu zuwa”.

Daga karshe Alhaji Mustapha A Sani yayi adduar Allah kawowa kasar Najeriya zaman lafiya.

Send:

Leave a Reply