Contact Info

Tsohon Gwamnan Kano Ya Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works Wato Malam Ibrahim Shekarau

Tsohon Gwamnan Kano Ya Ziyarci Kamfanin Afuwa Welding Works Wato Malam Ibrahim Shekarau.

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta tsakiya bugu da kari Sardauna Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ziyarci kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Shekarau ya ziyarci kamfanin ne a wannan rana ta Litinin tare da cincirumdon tawagarsa.

A yayin wannan ziyara tasa ya samu kyakyawar tarba daga shugaban kamfanin wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani tare da sauran ma’aikatan ko wanne sashe na kamfanin.

Haka zalika Eng. Mustapha A Sani ya zagaya da Dr. Kuma Malam Ibrahim Shekarau ko wanne lungu da sako na wannan kamfani.

Yayin zagayawa da shi ya yiwa wannan kamfani addu’a gami da sanya albarka a wannan katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Haka zalika Shekarau ya sami zarafin tattaunawa da Eng. Mustapha Abdullahi Sani sosai akan abubuwa da dama.

Haka zalika shi kansa Shekarau a lokacin da ya shiga kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works jinsa yayi tamkar a kasar China yadda yaga ake sarrafa karfe da kere-kere.

Daga karshe ya dauki hotuna na musamman tare da shugaban kamfanin da kuma hoton da suka dauka da sauran ma’aikatan kamfanin.

Send:

Leave a Reply