Contact Info

Tarihin Mustapha A Sani Mamallakin Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

An haifi Mustapha A Sani wato mamallakin katafaren Kamfanin Sarrafa ƙarfennan dake kasuwar Ƙofar Ruwa da dukkanin Arewacin Najeriya babu kamarsa, inda aka haifeshi a ranar 15 ga watan Janairu a shekarar 1974, yanzu haka yana da shekaru 48 kenan a duniya.

An haifeshi a wani gari da ake kira Lambu dake Ƙaramar Hukumar Tofa wato ɗaya daga cikin Ƙananan Hukumomi 44 da ake dasu a jihar Kano.

Ya fara karatunsa na addini wato addinin musulunci na Qur’ani da sauran littatafai tun yana ƙarami kuma ya halacci makarantu da dama. Sannan ya sauke littattafai da dama na addini.

Haka zalika a ɓangaren karatun zamani ya fara karatunsa a Katsinawa Primary School a Ƙaramar Hukuma Ungoggo, yana aji 3 aka mayar dashi Shahuce Primary School, ya yi karatunsa na gaba da Primary a ƙaramar Sakandire (Junior) a Shahuci, sannan kuma ya kammala karatunsa na babbar Sakandire (Senior) a Shahuci.

Alhaji Mustapha A Sani bai tsaya nan ba inda yayi karatunsa na gaba da Sakandire a F.C.E dake jihar Kano.

Mustapha A Sani da ake kira da Mustapha Afuwa ya fara sana’ar walda da sarrafa ƙarfe sama da shekaru 35.

Mustapha Afuwa ya ziyarci wasu ƙasashe inda daga ciki akwai Saudiyya inda ya sauke Farali sannan kuma yaje Umarah da dama. Haka zalika yaje ƙasar China inda ita kuma zuwanta duk a dalilin kamfaninsa inda ya ƙulla alaƙa dasu wajen sayo injinan sarrafa ƙarfe da sauran abubuwa kamar su fitila mai aiki da hasken rana da sauransu.

A ƙasar ta China Mustapha Afuwa ya ziyarci jihohi da garuwa da dama, inda daga ciki akwai Shanghai da Kenjing da Haifeng da sauransu.

Send:

Leave a Reply