Contact Info

Sokoto State University: Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction Yayimana Aiki na Ƙwarai Lokacin Gina Jami’armu a Sokoto.

Kamar yadda al’umma daga sassa daban-daban na Najeriya da sauran ƙasashe su ke ci gaba da mamaki a kan yadda ake ƙara sanar da su irin ayyukan da katafaren kamfanin sarrafa ƙarfennan da yayi shuhura a Najeriya wato Afuwa Welding Works And General Metal Construction, biyo bayan irin ayyukan kamfanin da ya gudanar a shekarun baya ake ta ganinsu a shafin yanar gizo na kamfanin.

A wannan lokacin kuma mun tsallaka zuwa jihar Sokoto wato jihar da kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar da ayyukansa masu nagarta lokacin da aka gina jami’a mallakin jihar Sokoto da ake kira da Sokoto State University.

Lokacin da Gwamna Aliyu Wamako ya fito da fiƙirar (Idea) ta ƙirƙiro jami’ar a shekarar 2008, sannan kuma a shekarar 2009 aka amince da kafa jami’ar, shine aka bincika a dukkanin kamfanonuwan da suke a Najeriya shin wanne za’a baiwa kwangilar aikin gine-gine da yin raftar ƙarfe (Metal Rafters) da sauran abubuwa, sai aka ga babu kamfanin da ya dace a baiwa aikin sai kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Wannan makaranta ta jami’a mallakin jihar Sokoto tana nan a garin Kasarawa kan titin Jega High Way dake jihar ta Sokoto.

Yayin gudanar da aikin gina makarantar kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya zubar da basirarsa wajen gudanar da aiki mai nagarta musamman yadda aka gudanar da raftar ƙarfe (Metal Rafters) mai kama da saƙar gizo-gizo da ake gani.

Shi kansa Gwamnan jihar Sokoto na wancan lokacin wato Aliyu Wamako ya jinjinawa kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wajen gudanar da aikin cikin nagarta da inganci.

Yin ayyuka masu nagarta da inganci ya sanya ako ina idan za a gudanar da ayyuka ake kiran kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction yake gudanar da ayyuka.

Idan za a iya tunawa wannan shafi na yanar gizo ya kawomuku ayyukan da kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar a jami’ar Bayero dake Kano musamman ginin Senate da jami’ar Yusuf Maitama Sule dake Kano da Husaini Adamu Kazaure Polytechnic dake Kazaure a jihar Jigawa da Kwaljin Sa’adatu Rimi dake Kano da Damp ɗin Obajana dake jihar Kogi da gidan gonar Alu (Alu Farm) dake Jigawa.

Sannan nan gaba za muci gaba da kawomuku sauran ayyukan da wannan kamfani ya gudanar a sauran sassan jihohin Najeriya.

Ga kwasan-kwasan (Courses) ɗin da jami’ar Sokoto take koyarwa.

Arabic Studies.

Biochemistry.

Biology.

Chemistry.

Computer Science.

Economics.

Education and Biology.

Education and Chemistry.

Education and Computer Science.

Education and Mathematics.

Education and Physics.

Educational Management.

English Language.

Geography.

Guidance and Counseling.

Hausa.

History.

Islamic Studies.

Mathematics.

Microbiology.

Physics.

Political Science.

Sociology.

Bisa wannan ayyuka masu nagarta da kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar a Sokoto State University ya sa mahukunta su ke sake yimasa jinjina da da fatan alkhairi.

Send:

Leave a Reply