Contact Info

Shugaban Kamfanin Afuwa Welding Works ya Kafa Sabon Tarihi a Kasar China da Najeriya da Babu Irinsa Wato Alhaji Mustapha A Sani.

Ta tabbata mamallakin kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato kamfanin da ya kware wajen sarrafa karfe a Najeriya kuma kamfanin da babu kamarsa a Arewacin Najeriya wato Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) ya kafa sabon tarihi.

Ya kafa wannan sabon tarihi ne a kasar China da kasarmu ta Najeriya da kuma sauran kasashen duniya.

Wannan tarihi ya kafa shine a wata ziyara da yaje zuwa kasar China wato kasar da Allah ya horewa basira wajen fannin kere-kere.

Wannan tarihi da Alhaji Mustapha A Sani ya kafa ya kasance yaje kasar China domin sayen wani injin lankwasa karfe mai wasu siffofi, amma akasamu akasi babu irin injin a kasar ta China, suna da mai kama dashi amma kuma bazai bayar da adadin irin abin da Mustapha A Sani ya kwatanta ba.

Bayan mutanen kasar China wato kamfanin da Mustapha Afuwa yaje suka zauna sukayi dogon nazari sannan suka ga ta yaya za’ayi su kirkirarwa Alhaji Mustapha A Sani kalar wannan injin da yake bukata, shine suka zauna suka keramasa shi kuma ya kawo shi kamfaninsa na Afuwa Welding Works And General Metal Construction dake Kofar Ruwa a jihar Kano.

Tarihin da Alhaji Mustapha A Sani ya kafa shine, tun bayan da wancan kamfanin na kasar China ya kirkiri kalar injin, a yanzu haka kasar China sun kama yin amfani da kalar injin a kasar su kuma suna sayar dashi ga sauran kasashen duniya.

Injin ya kasance shine na farko a Najeriya da kuma kasar China duk ta dalilin Alhaji Mustapha A Sani.

Sakamakon wannan abu da ya faru tun daga nan akasamu mutum daga Nahiyar Afrika kuma daga Najeriya ya kafa wannan katafaren tarihin wato Alhaji Mustapha A Sani wanda yake shine mamallakin kamfanin na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Send:

Leave a Reply