Contact Info

Salon Zanen Yankan Karfe Maikama da Zanen Bishiya Gami da Ado Mai Kayatarwa Akamfaninmu na Afuwa Welding.

Al’umma daga sassa daban-daban naci gaba da turo sakonni ta sassan shafukan sada zumunta na kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Mafiya yawan zanen karfen da suke gani na yau daban na gobe daban wanda hakan na matukar kayatar dasu kamar yadda suke bayyanawa.

A yanzu haka ga wani sabon salon aiki da wannan kamfani ya fitar a makonnan kuma aiki mai nagarta da bayar da sha’awa.

Wannan kalar ayyuka dai na zuwa ne bayan da shugaban wannan kamfani kuma wanda ya kware wajen fannin kirkira wato Alhaji Mustapha A Sani ya yake ci gaba da haska arewacin Najeriya ta fannin sarrafa karfe.

Idan masu bibiyar shafukanmu zasu iya tunawa ko yaushe muna cewa kamfanin Afuwa Welding Works kamfanine na sarrafa karfe kowanne iri ne.

Haka zalika a wani faifan bidiyo da muka saki a wannan rana ta Lahadi sannan muka sake shi a shafukan facebook da twitter a ranar Alhamis anjiyo yadda Mustapha A Sani yake wani bayani mai gamsarwa dangane da lankwasa karfe, wanda yace karfe kowanne iri ne idan an kawoshi kamfanin Afuwa Welding Works to za ayimasa yadda mutum yakeso.

Haka zalika wannan kamfani ne na kirkire-kirkire kuma kullum a cikin kirkirar sabon abu ake.

Send:

Leave a Reply