Contact Info

Sakon Barka da Juma’a Daga Mammalakin Kamfanin Afuwa Welding Works Alhaji Mustapha A Sani.

Yau ce ranar Juma’a wadda ake yi mata lakabi da Juma’atu babbar rana.

Kamar ko wanne mako a wannan rana ma shugaban kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction Eng. Alhaji Mustapha A Sani ya saba yin nasiha ko fadakarwa ko kuma tunatar da ‘yan uwa Musulmi akan wasu batutuwa.

A wannan rana dai Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’umma akan dukkanin abin da mutum zaiyi ya tuna cewa Allah yana kallonsa wato ya kamata mutum yaji tsoron Allah a cikin lamuramsa.

Mustapha A Sani ya kara da cewar matukar mutum zai kasance yana tunawa da Allah S.W.A to kuma yana yin biyayya ga dokokin Allah to tabbas ba zai tabe ba.

Send:

Leave a Reply