Contact Info

Sako Gami da Wasu Bayanai Akan Shigowar Sabuwar Shekarar 2024 Daga Eng. Mustapha A Sani.

Sako Gami da Wasu Bayanai Akan Shigowar Sabuwar Shekarar 2024 Daga Eng. Mustapha A Sani.

A yau Allah S.W.A ya nunamana farkon shekarar 2024 inda mu kayi ban kwana da shekarar 2023.

Kamar kowacce shekara a yau ma akwai jawabai gami da taya murnar shigowa sabuwar shekara daga shugaban kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Engineer Mustapha Abdullahi Sani.

“Jama’a assalamu alaikum, barkanmu da shigowa sabuwar shekara 2024, muna rokon Allah sada mu da dukkanin alkhairan dake cikin ta, sharrin dake cikinta kuma Allah kiyaye mu. Haka zalika kamfanin Afuwa Welding Works ya sake yiwa abokan huldarsa albishir na sake zuwa da sabon salon ayyuka a wannan kamfani da mukayo odar manyan injina daga kasar China”.

Eng. Mustapha A Sani ya kara da cewa tabbas akwai manyan tsaraba da kwastomomi za su yi farin ciki sosai da sosai.

Daga karshe Eng. Musta Daga karshe Eng. Mustapha A Sani ya yiwa kwastomomin wannan katafaren kamfani fatan alkhairi da fatan sake bijiro da salon ayyuka kala-kala masu inganci da nagarta.

Send:

Leave a Reply