Contact Info

Sabon Salon Walda: Muna Yin Walda Mai Nagarta da Inganci Gami da Launin Walda Maitafiya da Salon Fasahar Zamani.

Idan ana batun walda batu akeyi na wata sana’a wadda ta kwashe shekaru aru-aru kuma haryanzu ake gudanar da ita.

Saidai akanzo da salon yin aikin walda na zamani biyo bayan yadda ake samun ci gaba ta fannoni daban-daban misamman wajen yin amfani da fasahar zamani.

Shi kansa mamallakin katafaren wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction Alhaji Mustapha A Sani ya sha bayyanawa a kafafafen yada labarai idan anayin shira dashi cewa ya kwashe kusan shekaru 40 yana gudanar da wannan sana’a ta walda.

Kamfanin na Afuwa Welding ya kware wajen yin walda mai nagarta da inganci, hakance ma ta sanya ako da yaushe akanyi kwagance dashi wajen yin ayyuka masu inganci.

ALBISHIR:

A yanzu haka wannan kamfani yana sauya salon yin walda a ayyuka daban-daban wato walda mai tafiya da sabon salon fasahar zamani.

Wannan kamfani a kullum yana kan manufar nan ta fannin kirkire-kirkire, kuma kowanne irin aiki mutum yakeso a yimasa to babu makawa za’ayasa fiye da yadda ya kwatanta.

Send:

Leave a Reply