Contact Info

Sababbin Ayyuka Cikin Hikima da Kwarewa da Basira da Kuma Fasaha Daga Kamfanin Sarrafa Karfe Na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Sababbin ayyuka da kirkira cikin hikima da fasaha gami da kwarewa naci gaba da bayyanuwa a katafaren kamfanin sarrafa karfe na Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Shidai wannan kamfani ya kware wajen fannin kirkire-kirkire wanda babu irinsu gami da sabon salo na musamman da al’umma suke shan mamaki.

A yanzu haka dukkanin mutumin da ya je wannan kamfani zaiga abubuwa sun sauya sosai da sosai ganin irin abunuwa na musamman tamkar a kasashen waje.

A yanzu dai nesa ta matso kusa domin kuwa irin ayyukan da ake ganin ana gudanar dasu a kasashen waje to babu makawa ana gudanar dasu a wannan katafaren kamfani.

Tuni masu kwnanan kamfanin walda da sarrafa karfe suke ci gaba da zuwa wannan kamfani domin bayar da ayyukansu da kuma koyon yadda ake gudanar da wasu ayyukan da basusan irinsu ba.

Send:

Leave a Reply