Contact Info

Sa’adatu Rimi College Kano: Ayyukan da Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya Yimana Masu Inganci.

A wannan lokacin mun tsallako zuwa jihar Kano inda mu ka sauka a Kwalejin Sa’adatu Rimi dake Ƙaramar Hukumar Kumbotso a jihar Kano.

Wannan makaranta duk da an kwashe shekaru da kafa ta, amma akwai ayyukan da katafaren kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction ya gudanar a wannan makarana kuma ayyuka masu inganci da nagarta.

Domin kuwa akwai gine-gine da kuma raftocin ƙarfe na musamman masu kyau da nagarta da kuma inganci sannan kuma ga ƙarko.

Waɗannan ayyuka da ake gani ayyuka ne da suka ƙawata makarantar wanda dukkanin wanda ya gani tabbas zai san ayyuka ne masu nagarta.

Ita kanta Hukumar Makarantar ta yi jinjina da yabo na musamman ga wannan katafaren kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction wajen yin ayyuka babu ha’inci.

Wannan kamfani dai kamfani ne da dukkanin Arewacin Najeriya babu kamarsa, musamman yadda a yanzu al’ummar ƙasar waje da kansu suke gamsuwa idan sun shiga wannan kamfanin.

Domin kuwa akwai wani mutumin ƙasar China da yazo Kano yake neman inda za’a yimasa wasu ayyuka, bayan ya nema ya rasa yayi ta yawo a Kano, amma ana kawo shi kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction dake yana ganin manyan injina na musamman ya kama murmushi da dariya ta yadda ya san ayyukansa kamar an kammalasu an gama.

Kici gaba da bibiyar mu da waɗannan manhajoji domin ganin ayyukan wannan kamfani:

www.afuwaweldingworks.com

Facebook: Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Twitter: Afuwa Welding Works.

Send:

Leave a Reply