Contact Info

Saƙon Barka da Juma’a Daga Mustapha A Sani Wato Mustapha Afuwa.

A wannan rana ta Juma’a wadda akeyimata kirari da Juma’a Hajji babbar rana wato 28 ga watan Janairu, 2022.

Mamallakin katafaren kamfaninnan na sarrafa ƙarfe da yayi fice a Arewacin Najeriya Afuwa Welding Works And General Metal Construction wato Mustapha A Sani (Mustapha Welding), ya miƙa saƙonsa na Juma’a.

Ya miƙa saƙonne ga ‘yan uwa Musulmai inda yayi nasiha da jan hankali akan kalmar nan wato gaskiya.

Alhaji Mustapha A Sani yayi kira ga al’umma da su kasance masu kwatanta gaskiya da riƙon amana a dukkanin rayuwarsu ta yau da kullum.

“Ni Alhaji Mustapha ina kira da nasiha gami da jan hankali cewar mutane su zamanto masu yin gaskiya a al’amuransu da riƙon amana, domin dukkanin wanda ya zamo mai kwatanta gaskiya to babu makawa zaizauna lafiya da samun kwanciyar hankali”.

Daga ƙarshe Mustpha A Sani yayi addu’ar Allah Ya Zaunar da ƙasar Najeriya lafiya Ya kawo ƙarshen dukkanin wata fitina da kuma tashin hankalin dake faruwa a wasu sassan jihohin

Send:

Leave a Reply