Contact Info

Saƙon Barka da Juma’a Daga Mamallakin Kamfanin Afuwa Welding Works Alh. Mustpha A Sani.

Kamar kowanne mako yau ma Allah ya sake nunamana wannan rana ta Juma’a kuma rana mai daraja babba.

Haka zalika kamar ko yaushe mammalakin wannan kamfani Alhaji Mustapha A Sani (Afuwa Welding Works) ya sake miƙa saƙon barka da Juma’a ga al’ummar Musulmi kamar yadda ya saba.

A wannan rana dai Mustapha A Sani ya bayyana cewar.

“Sai mun kasance masu nuna godiya ga Allah S.W.A domin kuwa shine abin godiya, domin idan muna yimasa godiya tabbas zai bamu ninkin abin da ya bamu”.

Daga ƙarshe Mustapha A Sani yayi adduar dukkanin marasa lafiya na gida dana asibiti Allah Ya basu lafiya kuma Allah kawo sauƙin lamura a ƙasar nan ta Najeriya.

Send:

Leave a Reply