Contact Info

Saƙon Barka da Juma’a Daga Director General na Kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction.

Yau ma kamar kowanne mako Allah ya sake nunamana wannan rana ta Juma’a mai albarka wato ranar da ake yiwa laƙabi da babbar rana.

Kamar ko yaushe mamallakin wannan kamfani wato Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa) ya kan isar da saƙo na faɗakarwa ga al’ummar Musulmi da kuma saƙonnin tunatarwa.

A wannan rana ta Juma’a mai albarka Alhaji Mustapha ya bayyana cewar uzuri wani abu ne mai girma.

“Ya kamata mutane su gane cewa uzuri wani abu ne gagarumi kuma mai girma, sabo da haka mutane su dinga yiwa juna uzuri kafin su yanke hukunci domin rayuwa daman ita haƙuri ya fi yawa a cikinta”.

Wannan shine saƙon shugaban wannan kamfani na Afuwa Welding Works And General Metal Construction na wannan rana.

Send:

Leave a Reply