Contact Info

Ranar Juma’a: Saƙon Barka da Juma’a ga Al’ummar Musulmi Daga Alhaji Mustapha A Sani

Kamar kowanne mako mamallakin kamfanin Afuwa Welding Works And General Metal Construction Mustapha A Sani ya saba aika saƙon Juma’a ga al’ummar Musulmi.

A wannan rana ta 18 ga watan Feburairu ya sake yin nasiha ga al’umma domin a gyara.

Mustapha A sani dai ya bayyana cewar mutum ya kasance yana tare da abokai na gari kuma masu halaye na gari.

“Tabbas dukkanin wanda ya mori abokai na kirki to koda shawara zasu bashi lallai ta gari zasu bashi, shiyasa ya kamata iyaye su saka ido kan ‘ya’yansu domin ganin shin abokan da suke mu’amala dasu mutanen kirki ne? Idan iyaye su ka ga saɓanin haka to tabbas suyi maza su farga su ceto ‘ya’yansu tun kafin a sauyamusu tunani”.

Mustapha A Sani ya ƙara da cewar iyaye sai sun kasance suna yiwa ‘ya’yansu addua da roƙon Allah ya sanya albarka a rayuwarsu.

Send:

Leave a Reply