Contact Info

Northern Women Assembly: Mun Karrama M.D na Kamfanin Afuwa Welding Works Alhaji Mustapha A Sani Sakamakon Wasu Manyan Dalilai

Kungiyar Majalissar Mata na Arewacin Najeriya ta baiwa shugaban katafaren kamfanin sarrafa karfe na Arewacin kasar nan ta Najeriya lambar yabo.

Ta bayar da lambar yabon a yammacin jiya Talata ga Manajin Darakta na kamfain Afuwa Welding Works And General Metal Construction Alhaji Mustapha A Sani (Mustapha Afuwa).

Idan ba a manta ba daga farkon watan Janairu na sabuwar shekarar nan ta 2022 zuwa yanzu Alhaji Mustapha A Sani ya samu lambobin yabo masu yawa daga sassa daban-daban.

Wannan kungiya da ake kiranta da NOWA a takaice ta bayyana cewar akwai manyan dalilan da ya sanya ta karrama Alhaji Mustapha A Sani, kuma dalilan sune kamar haka:

1. Sakamakon kafa kamfanin Afuwa Welding Works Alhaji Mustapha A Sani ya samar da ilimi na musamman ga al’ummar Arewacin Najeriya wajen yin kere-kere.

2. Sannan zamanantar da wannan kamfani ya sanya matasa da yawa suna aiki da kuma ayyukan sabon salon fasahar zamani.

3. Al’ummar Arewacin Najeriya ta samu ci gaba da kafa katafaren wannan kamfani.

4. Kasar Najeriya tana alfahari da mamallakin wannan kamfani sannan kuma tana alfahari da gina wannan kamfani da babu kamarsa a Arewacin Najeriya.

Haka zalika wannan kungiya ta sake yabawa Alhaji Mustapha A Sani ganin yadda wannan kamfani yake tankar a kasar China.

Shima a nasa bangaren Alhaji Mustapha A Sani ya godewa Allah sannan ya yi godiya da yabo akan yadda wannan kungiya tayi hange wajen bashi wannan lambar yabo, sannan kuma yayi alkawarin zaici gaba da kare martabar Najeriya musamman Arewacin kasar ta Najeriya.

Send:

Leave a Reply